Sayyiduna Thabit bn Qays bn Shammas (ra) yana kwance awajen da yayi Shahada awajen yakin GHAZWATHUL YAMAAMAH (yakin da aka gwabza da Musaylamah)..Sai wani mutum daga cikin rundunar Musulmi yazo wucewa ta kusa dashi, Sai yaga cewar Garkuwar yakin da Thabit (ra) yake sanye da ita tana da kyau sosai. ta Qayatar dashi. Don haka sai ya dauke yayi tafiyarsa kawai abinsa.
Ana nan, Rannan sai wani Sahabi yayi mafarki da Thabit bn Qays yana ce masa: "ZAN GAYA MAKA WATA MAGANA. AMMA KAR KACE MAFARKI NE BALANTANA KA TOZARTAR DA ITA.
KAJE WAJEN ABUBAKAR (RA) KHALIFAN MANZON ALLAH (SAWW) KA GAYA MASA CEWAR: AKWAI WANE 'DAN WANE (YA FADI SUNAN MUTUMIN) GIDANSA YANA CHAN KARSHEN GARIN MADEENAH. SHINE YA SACE MIN GARKUWATA.
YA KAITA GIDANSA YA DANNETA DA WANI QATON DUTSE, KUMA YA 'DORA SIRDIN DOKINSA AKAN DUTSEN.
SANNAN KUMA ANA BINA BASHIN KAZA-DA-KAZA. KUMA SU WANE DA WANE DAGA CIKIN BAYINA, AGAYA MUSU CEWAR NA 'YANTASU".
Da wannan Sahabin ya farka daga barci sai yaje wajen Sayyiduna Abubakar ya shaidar masa labarin Mafarkin nan da yayi.
Nan take da aka je gidan Wancan mutumin sai aka ga dutsen. ana cirawa sai aka ga Garkuwar a inda ya boyeta.
Wannan yasa Sayyiduna Abubakrin (ra) ya zartar da sauran abubuwan da Mafarkin ya Kunsa.
In banda Sayyiduna Thabit bn Qays bn Shammas (ra) babu wani wanda yayi Wasiyyah acikin mafarki kuma aka zartar da wasiyyar tasa.
Babu wanda ya samu wannan karamar sai shi. (Allah shi Qara masa yarda).
Ya rasu ya bar 'ya'yansa Maza guda Uku sune:
Muhammad bn Thabit bn Qays.
Yahya bn Thabit bn Qays.
Abdullahi bn Thabit bn Qays.
Duk su ruwaici hadisai daga gareshi. Hakanan Sayyiduna Anas bn Malik (ra) shima ya ruwaici hadisai daga wajensa. Allah shi yarda dasu bai daya. Aameeen.
- Aduba USUDUL GHAABAH na Ibnul Atheer, akan tarjamar Thabit bn Qays (ra).