Allah ya yi wa tsohon ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Saud al-Faisal rasuwa 'yan watanni bayan da aka maye gurbinsa bayan shafe shekaru arba'in a kan mukamin.
Ya rasu yana da shekaru saba'in da biyar.
Kasancewar sa wanda ya fi dadewa a mukamin ministan harkokin waje, Yarima Saud ya yi suna a fagen siyasar duniya.
A zamanin rayuwarsa yarima Saud ya ce babban bakin cikinsa shine yadda shugabannin larabawa suka kasa cimma burin kafa kasar Falasdinawa.
Title :
Yarima Saud al-Faisal ya rasu
Description : Allah ya yi wa tsohon ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Saud al-Faisal rasuwa 'yan watanni bayan da aka maye gurbinsa bayan shafe...
Rating :
5