Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa har an kammala batun sayar da matatun man fetur har guda biyu a shekarar 2007, amma sai wanda ya gaje shi, wato marigayi Umaru Musa ‘yar’Adua ya soke batun saida matatun man saboda matsin lamba daga wasu al’ummar Nijeriya.
Janar Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyi a wani shirin da tabijin din Channels suke gabatarwa mai taken ‘Book Club’ a yau Laraba.
Ya kara da cewa tuni shahararren dan kasuwan nan Alhaji Aliko Dangote ya jagorancin wasu masu sanya hannun jaari suka biya dala milyan 750 na kudin matatun man fetur din guda biyu, sakamakon matsanancin rashin kudi da gwamnatin tarayya ta fuskanta a lokacin. Amma sai magajin nasa ya ki amincewa da sayar da matatun.
Obasanjo ya ce a yayin da ya tambayi marigayi ‘Yar’Adua dalilinsa na kin sayar da matatun man, ya fada masa cewa “na yi hakan ne saboda matsin lamba daga wurin wasu daga cikin al’ummar kasar nan. Sai nake ce masa wato matsin lambar da kake samu daga wurin al’umma ya fi muhimmanci fiye da matsalar rashin kudi da kasar take fama da shi?”
Obasanjo ya kara da cewa a yanzu ko dala milyan 250 ba za a sayi matatun man ba, saboda sun tsufa