Dan kwallon Arsenal Theo Walcott ya sabunta kwantaraginsa tare da kungiyar na karin shekaru hudu, inda zai dinga karbar fan dubu 140 a duk mako.
Dan wasan mai shekaru 26, ya zura kwallaye 50 a wasanni 208 da ya bugawa Arsenal tun lokacin da ya bar Southampton a shekara ta 2006 a kan fan miliyan 12.5.
Shi ma dan kwallon Spain, Santi Cazorla mai shekaru 30 ya sabunta kwantaraginsa da kulob din na karin shekaru biyu masu zuwa.
"Duka 'yan wasan zarata ne kuma suna da mahimmanci a gare mu," in kocin Arsenal Arsene Wenger.
A halin yanzu dai Walcott shi ne ya fi kowanne dan wasa dadewa a Arsenal.