Kungiyar Tarayyar Turai ta soma shawarwari wadanda za su kai ga hana bayar kudaden tallafin da ta ke bai wa kasar Burundi.
Wata babbar jami'ar harkokin kasashen waje a kungiyar, ta ce ta damu da tashin hankalin da ya faru gabanin zaben shugaban kasar Burundi, sannan kuma tana da shakkar cewar sakamakon zaben zai kasance abin da jama'a suke so.
'Yan adawa dai sun kauracewa zaben a ranar Talata.
Ana kuma tsammanin sakamakon zaben a hukumance a ranar Jumma'a.
Shawarar da Shugaba Nkurunziza ya yanke ta tsayawa takara a wani wa'adin mulki na uku ta ci karo da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanyawa hannu a kai a shekarar 2005, wacce ta kawo karshen yakin basasar kasa.