Ina ta sauri ,in gama wanke wanke dana ke
,domin in samu ,in tafi inda zani ,bana son in
je a makare .....nagama wanke wanke kenan
, ina tsane hannuna a jikin zani ......na janyo
kofin robar da bakin tukunya ya gama
yimasa fenti , na shanye kokon dake ciki
.....na sharche bakina da bayan hannuna
.....na gyara zaman dankwali na , gashina ga
yawa amma bbu gyara ,in ka ganni kamar
mahaukaciya sabuwar kamu , ga baqar
kazanta a tattare dani ,toh ba dole ba ,muna
fama da rashin ruwa , ga rashin maggin
zaman duniya .....na fada dakin da innata
take ,nace 'inna zan wuce ,ki tayani da
addu'a ...inna ta dubeni cike da kulawa 'Allah
ya tsare ya kuma bada sa'a 'NADIYA' ......nace
'amin inna ' ,na shuri silifas mai kama da
fate na fice sai gidan sarki dake nan bayan
layin mu ba nisa ..........
NADIYA BUBA sunana , mu uku iyayena suka
haifa , wato ni da kannena guda biyu sabeer
da safah , mahaifina ya rasu a dalilin gini da
ya fado mai ,yan uwansa sun gujemu ,ga
mahaifiyata itama tana fama da rashin
dangi, domin ba'a son rabemu ko kadan , ko
biki ko suna mukaje ....sai an nuna mana
TSANA ,saboda rashin kimtsi (rashi ne ya
jawo haka ) ,a yanzu shekarata goma sha
bakwai , a daddafe nagama secondary , da
taimakon Allah, da kuma yan dabarun sana'a
da mukeyi acikin gida irinsu wankau ,surfe
da kuma kayan miya , gida dai ko in ce
shinge da muke ciki alhamdulillah namu ne
na kanmu .........nasamu aiki a gidan sarki ta
dalilin wata aminiyar inna da yake ita ma
tana aiki acan ........
Mu goma aka dauka aiki ,maza uku mata
bakwai,bayan an bamu uniform din mu , ni
har wanka aka umarceni in je inyi domin
kazantar dake tattare dani ,ALLAH ya tsaga
da rabon zan samu aikin ne ........domin a
yadda shugaba mai raba aiyyuka ,tace ' ni
zan kula da bangaren YAREEMA FUDAIL ne
,irinsu shara ,wanke toilet da kuma kai ma
breakfast ,lunch nd dinner ,inzo 7am in bar
fada 7pm , albashina kuwa 30k , shar! dani
yar gidan marigayi buba magini......... ......