Ansha yaða jita-jitar Sadiya Gyale suna soyayya da jarumi Baballe Hayatu tun kafin Sadiya Gyale tayi aure, sai da jarumi Baballe Hayatu ya wayarwa jama'a kai tsakaninsa da Sadiya Gyale ba soyayya bace kaunace.
Ankara tabbatar da haka awajen walimar ðaurin auren Sadiya Gyale, inda jarumi Baballe Hayatu shiya ðauki nauyin komai.
Baballe Hayatu ya gayawa wakiliyar Maryam Hotoro tsakaninsa da Sadiya Gyale kamar haka:
Ni Sadiya Gyale ta zama kamar yar uwata, sabida zaman mutunci da mutunta juna. Tana ganin girma ni kuma na ruke girmana. Tarihin haðuwarmu da Sadiya yanada tsawo, tun bayan na sakata acikin fim ðin dana bada Umarni mai suna 'Gyale', wanda sunan fim ðin yabita tun anan muka soma mutunci da Sadiya Gyale. Ina bata shawara itama tana bani shawara. Ko wannan wanda ta aura saida ta nemi izninina akan fara soyayyarsu, tunda naga mutumin kirkine saina bata shawarar auransa. Yanzu haka tana gidan mijinta hankali kwance ba abinda yadameta.
Nasha cece-kuce bayan auren Sadiya Gyale, domin wasu gani sukeyi tsakanina da ita soyayyace yaudararta kawai nayi. Nagode Allah daya cikawa Sadiya Gyale burinta, kullum in muna magana da Sadiya Gyale burinta addu'arta bata wuce Allah kabani mijin aure. To Allah maji roko yacikawa Sadiya burinta.
Dan haka matsayin Sadiya Gyale awajena ya wuce na saurayi da budurwa yafina abokiyar kasuwanci ta zama kamar yar uwata inji Baballe Hayatu.
Title :
Tsakanina Da Sadiya Gyale--Baballe Hayatu
Description : Ansha yaða jita-jitar Sadiya Gyale suna soyayya da jarumi Baballe Hayatu tun kafin Sadiya Gyale tayi aure, sai da jarumi Baballe Hayatu ya w...
Rating :
5