Wasu majiyoyi da ke da kusanci da kungiyar Taliban ta Afganistan sun ce kungiyar ta nada sabon shugaba bayan rasuwar Mullah Omar.
Sabon shugaban dai shi ne tsohon babban kwamanda na biyu na kungiyar ta Taliban, watau Mullah Mansour.
Sai dai, majiyoyin sun shaidawa manema labarai cewa nadin da aka yi wa Masour ya bai wa sauran manyan kwamandoji na kungiyar haushi.
Shugabannin za su a so ace dan marigayi Omar ne ya gaji mahaifinsa.
Kazalika, Pakistan ta ce an dage tattaunawar zaman lafiya zagaye na biyu tsakanin gwamnatin Afghanistan da kuma kungiyar ta Taliban bayan bukatar da kungiyar ta gabatar game da haka.