Sabon dan wasan da Manchester City ta saya Raheem Sterling ya ci mata kwallo a wasan da ta doke Roma a Melbourne ranar Talata.
Sterling mai shekaru 20, ya zura kwallon ne a minti uku da fara buga wa sabuwar kungiyarsa a wasan sada zumunta.
Dan wasan mai shekaru 20, ya koma City ne kan kudi £49m daga Liverpool a ranar 14 ga watan Yuni.
Sterling ya yi wasan ne ta bangaren hagu daga gaba tare da David Silva da Kelechi Iheanacho, kafin a sauya shi bayan da aka ta fi hutu.
Shi ma Iheanacho ya ci kwallo a karawar da suka tashi 2-2, kafin City ta samu nasara a bugun fenariti da ci 5-4.
Wannan shi ne wasan farko da City ta buga a gasar Champions Cup kafin ta fafata da Real Madrid a ranar Juma'a.