Tsohon kyaftin din Liverpool, Steven Gerrard ya ce Raheem Sterling ya ba shi kunya.
A cewarsa ya kamata Liverpool ta sauya tunaninta kuma ta saka Jordan Henderson gaba domin samun nasara.
Sterling bai yi atisaye ba saboda rashin lafiya sannan yanason barin Liverpool inda Manchester City ta ba da tayi a kansa.
A yanzu dai an nada Henderson a matsayin kyaftin din Liverpool.
"Jordan na biyayya ga kungiyar kuma ina masa fatan alheri," in ji Gerrard.