Rundunar sojin Najeria ta ce ta ceto karin fararen hula 59 wadanda 'yan Boko Haram suka kama a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Rundunar ta kuma fitar da sabbin hotuna da ke nuna yadda dakarunta ke gwagwarmaya a fagen daga a yakin da suke yi don murkushe mayakan Boko Haram.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Kanal Kukasheka Usman, ya fitar ta ce a wani sabon hai da aka kai wa mayakan Boko Haram an lalata sansanoninsu da ke Chogori da Shantumari a jihar Borno.
A yayin da aka kai wasu hare-haren a kan masu tayar da kayar bayan da sun ta fitowa daga ramuka suna tserewa.
Kazalika, dakarun bataliya ta 151 ta rundunar hadin gwiwa sun kaddamar da wasu hare-haren a sansanonin masu tayar da kayan bayan Kashingeri da Wale da kuma Kushingari a ranar Alhamis.
A yayin hare-haren dai an kashe masu tayar da kayan bayan da dama.