Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa mutane akalla takwas sun mutu, wasu fiye da dari kuma suka jikkata, sakamakon fashewar wata tukunyar sinadari a wata matatar ruwa a Jos babban birnin jihar, a yau.
Hukumomi dai sun bayyana cewa fashewar ba ta da nasaba da bam ko kuma wani makami, wani sundukin sinadarin Chlorine ne da ake amfani da shi wajen tace ruwan sha, ya fashe kuma bindigar da sundukin ya yi, ta haddasa fitar sinadarin mai karfin gaske, kana dimbin mutane suka shaka ya kuma toshe masu hanyar shakar iska.
Mahukuntan dai sun bayyana cewa babu wata illa da fashewar ta yi wa ruwan na sha don haka kada jama'a su ji fargabar amfani da ruwan na famfo ba.