Manzon Allah (saww) ya kasance yana da rawuna kala-kala. yakan sanya Baqin rawani. Awasu lokutan kuma yakan sanya fari, ko kuma wata kalar daban.
JABIR BN ABDILLAH AL-ANSAARY (RA) ya ruwaito mana cewar :
"ARANAR FAT-HU MAKKAH (YAQIN BUDE GARIN MAKKAH) MANZON ALLAH (SAWW) YA SHIGO GARIN YANA SANYE DA BAQIN RAWANI. BA TARE DA IHRAMI BA"
(Aduba Sahihu Muslim hadisi mai lamba 1358).
Kuma Manzon Allah (saww) ya kasance yakan sanya jelar rawanin ta zamto tsawon yatsa hudu sannan ya jefa ta bayansa atsakanin kafadunsa. Kamar yadda sahabin nan AMRU BN HURAITH (RTA) Yake cewa:
"KAMAR NI INA KALLON MANZON ALLAH (SAWW) AKAN MIMBARI ALOKACIN DA YAKE KHUTUBAH YANA SANYE DA BAQIN RAWANI, KUMA YA JEFA GEFEN RAWANIN ATSAKANIN KAFADUNSA"
(SAHIHIN HADISI NE. Aduba Sahihu Muslim hadisi na 1359).
Kamar yadda shima ABDULLAHI BN UMAR (RTA) ya ruwaito cewar Manzon Allah (saww) ya kasance idan ya daura rawani yakan saki rawanin ta tsakanin kafadunsa.
Hakanan shima Sayyiduna Abdullah bn Umar din ya kasance yana yi. Har ma 'ya'yansa ALQASIM DA SAALIM (RA).
Kamar yadda yazo acikin Littafin SUNANUT-TIRMIDHY hadisi na 1736:
Wata rana Annabi (saww) ya Aiki Sayyiduna Abdurrahman bn Auf (rta) zuwa wajen wani Yaqi, Sai yaganshi ya fito sanye da wani baqin rawani.
Sai nan da nan Annabi (saww) ya kunce masa wannan rawanin sannan ya sanya hannayensa masu Albarka ya nada masa wani FARIN RAWANI.
(hakim ya ruwaito hadisin acikin MUSTADRAK, HADISI mai Lamba 8623.)
DAGA ZAUREN FIQHU
Ya Allah ka Qara salati da Sallama ga Annabinmu adadin numfashin halittunka acikin kowacce Kifatawar ido sau adadin dukkan halittun.