Wasu majiyoyi na gwamnatin kasar Afghanistan sun ce shugaban 'yan kungiyar Taliban Mullah Omar, ya mutu.
Sai dai kungiyar ba ta ce komai a kan wannan ikirari da majiyoyin suka yi ba.
Majiyoyin daga hukumar leken asirin kasar sun ce Omar ya mutu ne shekaru biyu zuwa uku da suka wuce.
Babu cikakken bayani a kan dalilin mutuwar sa.
Wani mai magana da yawun kungiyar ta Taliban da manema labarai suka tuntuba ya ce nan gaba kadan ne za su fitar da sanarwa a kan batun.
A baya dai an sha bayar da rahotannin da ke cewa Mullah Omar ya mutu.
Amurka ta sa diyyar $10m ga duk wanda ya taimaka aka kama Omar
Amma wannan shi ne karon farko da hukumomin kasar ke tabbatar da mutuwar sa.
Mullah Omar shi ne ya jagoranci Taliban wajen yin nasara a kan kungiyar da ke hamayya da su a yakin basasar da ya faru bayan janyewar dakarun Tarayyar Soviet daga kasar.
Kawancen da ya kulla da shugaban kungiyar al-Qaeda leader Osama Bin Laden ne ya sa Amurka ta jagoranci mamayar da aka yi wa Afghanistan a shekarar 2001, bayan harin da aka kai a biranen New York da Washington a ranar 11 ga watan Satumba na shekarar.
Amurka ta sa diyya $10m ga duk wanda ya taimaka ta kama Mullah Omar, kuma tun daga lokacin ne ya rika buya.
'Yan Taliban sun kwashe shekara da shekaru suna fitar da sakonni da suka cewa sun fito ne daga Mullah Omar.