Kwana daya bayan da 'yan kungiyar Taliban suka tabbatar da mutuwar shugabansu, Mullah Omar, akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewar shi ma wani jigo a wata kungiyar 'yan gwagwar maya ya rasu.
Jalaludin Haqqani, shugaban kungiyar Haqqani, abokin kawance ne na kut da kut na kungiyar Al-Qaeda da kuma kungiyar Taliban.
Wani wanda ya ke da kusanci da kungiyar, ya ce Haqqani ya mutu ne sakamakon rashin lafiya da yayi a shekarar da ta wuce.
Sai dai wani babban jami'i ya ce lamarin ya faru ne shekaru shida da suka wuce.
Kungiyarsa wacce ta ke kasar Pakistan, a da tana cikin tawagar 'yan kungiyar Taliban a tattaunawar zaman lafiya da aka yi a farkon watan Yuli na wannan shekarar.
Tuni aka sanarda dan Jalaludin watau Sirajudin Haqqani a matsayin mataimakin shugaban 'yan kungiyar Taliban.