A yau ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kwanaki biyu Jamhuriyar Kamaru inda zai gana da takwaransa na Kamaru shugaba Paul Biya.
Wannan ziyarar ta na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar Boko Haram ke kara kai hare-haren kunar bakin wake a lardin arewa mai nisa na Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.
Rahotanni sun ce batun tabbatar da tsaro a tsakanin kasashen biyu har da yankin tafkin Chadi shi ne zai kankane tattaunawar da Shugabannin biyu za su yi.
A wani bangaren kuma, shugabannin biyu za su dawo da huldar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu wadda tayi sanyi tun lokacin da batun rashin tsaro ya kunno kai.
Baya ga kasar China, Najeriya ta kasance kasa ta biyu da take shigo da kayan haja Kamaru.