Mahukunta a kasar Saudi Arabia sun ce sun cafke fiye da mutane dari hudu da ake zargi 'yan kungiyar I-S masu da'awar jihadi ne.
Ba dai a bayar da wasu cikakkun bayanai ba.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ya ce an dakile yunkurin kai hare-hare da dama a kasar.
Sun hada da da yunkurin hallaka wasu dakarun tsaro, da kuma harin kunar bakin wake a masallatai.
Kungiyar ta I-S ta ce ita ke da alhakin kai harin tagwayen bama-baman nan kan masallatan musulmai yan Shi'a a gabashin kasar cikin watan Mayu--inda mutane 25 suka hallaka.