Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga kungiyar likitocin Nigeria masu neman kwarewa da su janye yajin aikin da suke yi yanzu haka.
Ya ce yajin aikin na su a wannan lokaci ba komai zai haifar ba illa karawa marasa lafiya tsananin wahala ne kawai.
Sarkin ya ce matukar ba a nada ministoci ba to zai yi wuya gwamnati ta saurare likitocin, domin haka ya ce yajin aikin ba zai taimaka musu kai wa ga biyan bukatunsu ba.
Likitoci masu neman kwarewa dai sun kwashe makonni suna yajin aikin a Najeriya saboda suna so a kara musu albashi da inganta yanayin wurin aiki da kuma neman karin kayan aiki.