Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya
amince da nadin sabobbin manyan jami'an
tsaron kasar.
A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar,
Femi Adesina ya fitar, ta ce an nada 1. Manjo Janar
Abayomi Gabriel Olonishakin a matsayin babban
hafsan hafsoshin tsaron kasar.
2. Sai kuma Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai a
matsayin hafsan dakarun sojin kasa na kasar.
3. Sanarwar ta ce sabon hafsan dakarun sojin
ruwan kasar shi ne Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe
Ibas
4. A yayinda aka nada Air Vice Marshal Sadique
Abubakar a matsayin babban hafsan sojin saman
kasar.
Sauran wadanda shugaba Buhari ya nada a
bangaren tsaron, sun hada da 5. Air Vice Marshal
Monday Riku Morgan a matsayin babban jami'in
kula da bayanan sirri na tsaro a kasar 6. Da kuma
Manjo Janar Babagana Monguno a matsayin mai
bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin
tsaro.