A Najeriya, yayin da 'yan majalisar dattawan kasar ke komawa bakin aiki ranar Talata, alamu na nuna cewa takaddama ka iya barkewa bisa zargin sauya kundin tsarin tafiyar da majalisar da wasu suka ce an yi.
Sanata Kabir Marafa, daya daga cikin 'yan majalisar ta dattawan, ya shaida wa manema labarai cewa wasu tsirarun mutane sun sauyawa kundin tsarin zauran fasali domin ya yi dai da muradinsu na kasancewa jagororin majalisar.
Ya ce kawo yanzu babu wanda ya san iya adadin sauye-sauyen da aka yi wa kundin sai an yi cikakken bincike.
Wannan dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan majalisar ta dattawa suke komawa bakin aiki bayan kwashe makonni biyar suna hutu.
Ana sa ran wannan batu shi ne zai mamaye zaman majalisar na ranar Talata, al'amarin da wasu ke ganin ka iya fama ciwon da ke damun majalisar.
Tun dai bayan da tsohon gwamnan jihar Kwara da ke arewa maso tsakiyar kasar, Sanata Bukola Saraki da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu suka yi nasarar darewa a kan kujerun shugaban majalisar da ta maitaimaka masa, rikici ya yi kamari a zauran.
Rundunar 'yan sandan kasar ta gudanar da bincike dangane da batun sauya kundin ta kuma nemi ofishin ministan shari'a da ya bayyana shin ko yin hakan ya saba wa dokokin kasa.
'Yan majalisar wakilai ma suna fama da takaddama
A nasu bangaren, 'yan majalisar wakilan kasar za su koma bakin aiki ne a dai dai lokacin da suke rikici kan shugabancin majalisar.
Rikicin ya barke ne sakamakon zaben da aka yi wa Honourable Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisar, sabanin wanda jam'iyyar APC mai mulki a kasar ta ce a zaba, Honourable Femi Gbagjabiamila.'y