Rahotannin daga garin Ile-Ife na jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa basaraken gargajiyar nan na kasar yarabawa,Oba Okunade Sijiwade wanda shi ne mai rike da sarautar Oni na Ife ya rasu a daren Talata.
Makusantan mamacin wadanda suka sanar da rasuwar sun ce Oba Sijiwade mai shekaru 85 ya rasu ne a wani asibiti da ke Birtaniya bayan ya yi jiyya.
Basaraken dai ya kwashe shekaru 35 akan karagar mulki bayan dare kujerar ta Oni a shekarar 1980.
Oba Ounade ya kasance na hannun damar tsohon sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.