Rundunar sojin Chadi ta ce ta kashe fiye da mayakan Boko Haram 100 cikin makonni biyu da suka gabata a wani gumurzu da ake yi a tafkin Chadi da kewaye.
Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin.
Kungiyar Boko Haram ta fara kai hare-harenta ne a Najeriya amma yanzu ta kutsa wasu kasashen da ke yankin.
A ranar Alhamis ne majalisar dokokin Chadi ta kada kuri'ar mai do da hukuncin kisa a kan 'yan ta'adda, bayan da aka soke hukuncin watanni shida da suka gabata.
'Yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula sun soki dokar yaki da ta'addancin, suna masu cewa za a yi amfani da ita ne wajen tauye 'yancin fararen hula.