Raheem Sterling ya ce ya samu kwanciyar hankali, bayan da ya kammala koma wa Manchester City daga Liverpool.
Sterling ya koma Ettihad ne da murza leda kan kudi £49m, kuma a shirye yake ya kalubalanci lashe manayan kyautuka.
Dan kwallon ya ce zai kara samun goge wa a City, bayan da ya zama dan wasan Ingila da aka saya mafi tsada a tarihi.
Sterling ya ki amincewa da tayin tsawaita kwantiraginsa a Anfield duk da sai a shekarar 2017 zai kare.
Tun da fari Manchester City ta taya Sterling karo biyu a inda Liverpool ta ki ta sallama, kafin ta amince da tayi na uku.
Sterling ya koma Liverpool ne daga kulob din QPR a shekarar 2010.