Shugaban Amurka, Barack Obama, ya ce ya zuwa yanzu ya gamsu da alkiblar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya a gaba.
Mr Obama ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar da takwaransa na Najeriya ya kai masa a fadar White House ranar Litinin.
Shugaba Obama ya ce kasarsa za ta hada gwiwa da Najeriya domin murkushe 'yan kungyar Boko Haram da kawar da cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa Najeriya tana da matukar muhimmanci wajen ci gaban duniya, yana mai cewa hada gwiwa da ita zai sa a samu dawwamammen zaman lafiya a nahiyar Afirka.
A nasa jawabin, Shugaba Buhari ya yabawa Amurka bisa jajircewar da ta yi wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a watannin Maris da Afrilu, wadanda suka yi sanadiyar zaman sa shugaban kasa.
Ya kara da cewa ba da ban jajircewar da Amurka ta yi ba, da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ba za ta yarda da shan kaye ba.
Ya nanata kudurinsa na shawo kan matsalolin tsaro da magance cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga 'yan kasar.