Kamfanin man fetur na Nigeria, NNPC ya sanar da cewar matatun mai na Fatakwal, da Warri sun soma aiki bayan garambawul da aka yi musu.
Sanarwa daga NNPC ta ce a yanzu, matatar mai ta Fatakwal ta soma tace litar mai miliyan biyar a duk rana a yayinda ake samar da litar mai miliyan uku da rabi a kullum daga Warri.
NNPC ya ce matatar mai ta Fatakwal na aiki kashi 60 cikin dari wajen tace mai ganga 210,000 a kullum, yayinda matatar mai ta Warri ke aiki kashi 80 cikin dari na tace mai ganga 125,000.
Kamfanin ya ce ma'aikantansa na cikin gida da injiniyoyinsa ne suka gudanar da ayyukan da suka sa matatun man suka koma bakin aiki.
Nigeria na shigar da miliyoyin lita na tataccen man fetur daga kasashen waje saboda matatun man kasar ba sa aiki.