Manchester United ta kamalla dauko dan kwallon Jamus, Bastian Schweinsteiger da kuma dan Faransa Morgan Schneiderlin.
Schweinsteiger mai shekaru 30, ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru uku a kan fan miliyan 14.4 daga Bayern Munich.
Schneiderlin mai shekaru 25, shi ma ya koma United ne daga Southampton a kan fan miliyan 25.
Tuni United ta dauko Memphis Depay da kuma Matteo Darmian.
Schweinsteiger ya yi kwallo a karkashin kocin United Louis van Gaal a lokacin ya na jan ragamar Bayern daga 2009 zuwa 2011.
Title :
Man United Su Sayi Schweinsteiger da Schneiderlin
Description : Manchester United ta kamalla dauko dan kwallon Jamus, Bastian Schweinsteiger da kuma dan Faransa Morgan Schneiderlin. Schweinsteiger mai sh...
Rating :
5