TAMBAYA TA 1652
*********************
Assalamu Alaikum Malam sannu da kokari Allah yasaka maka da alkhairi, Malam don Allah inason a ansa man tambayata?
Daga wata baiwar Allah
Malam idan mace na haila zata iya karatun alqur'ani Application a waya?
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Eh ya halatta mace mai haila ta bude Application mai dauke da Alqur'ani (irin na cikin wayoyin Android Android din nan).
Kuma ya halatta tayi tilawar guraren da ta haddace (Wato ba tare da ta taba takarda ba). Bisa fatawar Maluman Mazhabin Malikiyyah.
Amma bai halatta ta dauki Takardun Alqur'ani, ko Allon da yake dauke da rubutun Alqur'ani ba.
Wasu Malaman suna ganin cewar zata iya daukar Alqur'anin idan aka kunsheshi acikin wani abu. Amma magana mafi inganci ita ce akiyaye kar a dauka din. Saboda Martabar Alqur'ani