TAMBAYA TA 1648
*******************
Assalam alaikam Allah ya taimaki malam ya saka mai da gidan Aljannah, malam mamata ce tadaina gani dazun, shine muke bukatar ataimaka mana da magungunan da zamu nema da shawarwari da kuma addu,ah Daga dalibinka Ibrahim Ibrahim nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Ku nemi ruwan zam zam da kuma Man Zaitun ingantacce. Kowanne daga cikinsu ku tofa masa wadannan surorin kamar haka:
1. Fatiha 7.
2. Ayatul kursiyyi kafa uku.
3. Ayatush shifa'i gaba dayansu kafa 7.
4. "Allahu waliyyul ladheena aamanu Yukhrijuhum minaz Zulumati ilan Noor" (kafa bakwai).
5. QUL HUWALLAHU 11.
6. Falaki da Naasi Qafa 11.
7. "Allahumma Rabban Naas azhibil Ba'as washfi antash Shaafee. La SHIFA'A ILLA SHIFA'UKA. SHIFA'AN LAA YUGHADHIRU SUQMAN". Kafa uku.
8. Salatun Nabiyyi (saww) gwargwadon iko.
Kullum idan zata kwanta barci ku rika diga mata Man zaitun din nan acikin idanunta. Da rana kuma ku rika diga mata zamzam din. kuma tan wanke fuskarta dashi.
In sha Allahu kafin wani lokaci Allah zai warkas da idanunta da Qarfin ikonsa da falalarsa.
WALLAHU A'ALAM.