Assalm alaik malan ya gida ya yara? Allah ya saka da alkhairi. ..malan sister na ce take fama da menstrual pain sosai kafin ta fara kuma sai tayi 2 months batayiba amma in ta tashi yi sai yazo da yawa. Amma taje hospital suka bata premolut N sannan yazo. Kuma bata taba yin family planning ba. Dan Allah malan meye solution din.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Shi irin wannan matsalar rikicin jinin al'adar yana da wasu dalilai da dama wadanda suke haifar dashi.
- Wani lokacin irin chututtukan da ake dauka yayin Jima'i suna haifar da irin wannan.
- Wani lokacin kuma kwayoyin chuta (Infection, viruses) idan sun shiga cikin mahaifar mace sukan haifar da irin wannan.
- Wani lokacin kuma tashin hankali da rashin samun nutsuwa sukan haifar da irin wannan.
- A yawancin lokuta kuma, idan mace tana tare da shafar Shaitanun Aljanu sukan yi ajiya acikin farjin mace ko mahaifarta, asanadiyyar haka zata rika samun matsalar jinin haila, da kuma jin zafi yayin saduwa da mijinta.
Akwai bukatar ta sake komawa asibiti wajen manyan likitoci suyi mata duk test din da zasu iya yi. Idan ba'a samu dacewa ba, Sai taje ayi mata rukyah a Asibitin Musulinci mafu kusa da ita, kuma ta nemi magunguna kamar haka:
- Man Albabunaj (Hemani ko MISRA).
- Man Zaitun na ainihi.
- Man Habbatus Sauda (Hemani ko Misra).
Ta gaurayasu waje guda a karanta ayatur Rukyah, ayatush shifa'i, da kuma "WA LAHU MA SAKANA FIL LAILI WAN NAHAAR" X 7.
Ta rika shan cokali guda safe da rana da yamma sannan ta rika shafawa a mararta. In sha Allahu zata rabu da wannan ciwon da rikicin jinin har abada da izinin Allah Madaukakin Sarki.
WALLAHU A'ALAM.