Wani mutumine zai mutu sai ya
tara 'ya 'yansa guda goma yace: "inna
mutu kuje
wajen abubuwa guda hudu zasu fa'da
maku wasiya ta" Abubuwa guda hudunnan sune:
KIYASHI, MACIJI,
BALBELA, da HAWAINIYA.Bayan
mutuwarsa sai suka
kwashe jiki suka je wajen KIYASHI. Sai
kiyashi ya kada baki yace masu: 'wasiyar
mahaifinku a
guna itace'
"nidai da kuke gani 'dan karamine
amma duk abinda
nasamu sai nakira 'yan'uwana mun
'dauka zuwa gida. Saboda haka, dukkanku sai ku
koyi
wannan hali nawa.
Kuzama masu hadin kai ba masu hadin
baki ba."Da
fitatrsu a gun kiyashi sai suka je gun
MACIJI. Sai maciji yace masu: 'kunga jikina dai
yana da
kyau, amma
kowa yana tsoron harshena.' Don haka,
ku guji
harsunan ku.Bayan fitarsu daga gun
maciji, sai suka je wajen HAWAINIYA. Dazuwan su
sai
hawaiya yace
masu: 'kamar yanda kuka sani dai ni
banda sauri
wajen tafiya, amma nakan chanza duk
kalan abinda nakeso kuma inyi tafiya iya tsawon
yanda nakeso. Don
haka ku guji hanzari arayuwa.'Fitarsu
keda wuya daga
gun hawainiya, sai suka je gun BALBELA.
Balbela kuwa yace dasu: 'nidai wata halittace
wanda
bana kiwo a
cikin gari sai a daji, kuma bayan shanu
nake hawa
saboda insuna tafiya cikin ciyayi, fara
suna tashi. Sai nikuma in kama inci har in qoshi
in
dawo gida. Saboda
haka, a rayuwa dole sai kabi wani kafin
kaima kazama
wani