Lang wani saurayi ne mai farin ciki, ba shi da kome sai wani bijimi da garma guda. Ko wace rana ya yi aikin noma a cikin gona, da ya koma gida sai ya dafa abinci da kuma wanke tufafi da kansa. Amma wata rana, abin ban mamaki ya faru.
A ran nan da Niu Lang ya shiga kofar gida, sai ya ga an riga an tsabtace dakinsa, kuma an wanke dukan tufafinsa. Har ma akwai abincin da aka dafa a kan teburi. Amma, ba wanda ke cikin gida. Niu Lang ya ji mamaki kwarai, bai san dalilin da ya sa haka ba.
Bayan haka, kwanaki da yawa sun wuce, kuma ko wace rana da Niu Lang ya koma gida, sai ya ga tsabtatacen daki da abincin da aka dafa masa. Niu Lang yana so ya yi bincike kan abin da ya faru. Sai wata rana, da sassafe ya bar gida kamar yadda kullum ya kan yi a ko wace rana. Amma bai nufi gona ba. A madadin haka, ya boye a gaban gidansa, yana leken abin da zai faru.
Ba da dadewa ba, sai ya ga wata budurwa mai kyaun gani. Ta shiga gidansa kai tsaye, ta fara aikin gida. Ganin haka, Niu Lang ya fito daga wurin da ya buya, ya tambaye ta cewa, ‘An gaishe ki budurwa mai kyaun gani, me ya sa kike taimako ni wajen aikin gida ?’ Budurwar ta razana, kuma ta ji kunya. Ta yi magana da karamar murya, ta ce, ‘Sunana Zhi Nu. Na ga kana zama cikin kadaici da shan wahala, shi ya sa na zo taimake ka.’ Niu Lang ya ji murna kwarai da gaske, sai ya ce, ‘ Sai ki aure ni, bari mu yi aiki tare da zama tare, mu debe wa juna kewa.’ Zhi Nu ta yarda. Daga baya, Niu Lang da Zhi Nu sun yi aure sun zama miji da mata. Ko wace rana, Niu Lang ya je aiki a cikin gona, Zhi Nu sai ta yi aikin saka a cikin gida. Bayan shekaru, sun haifi yara 2, namiji daya, mace daya. Suna jin dadin zamansu.
Suna nan cikin halin, sai wata rana, ana iska kuma ana hadari a can sama. Aljanu biyu sun sauka daga sama, sun zo gidan Niu Lang. Sun sanar da shi cewa, Zhi Nu jika ce ta sarkin aljanu. Shekarun da suka wuce ta bar gida ba tare da izini ba, daga baya sarkin aljanu na ta kokarin nemanta. Daga baya, aljanun 2 sun kama Zhi Nu, sun kai ta sama.
Niu Lang ya rungume yaransa, yana bakin ciki kwarai. Ya lashi takobin cewa zai nemi matarsa, da kuma dawo da ita gida. Amma, yaya mutum zai iya hawa can sama ?
Ganin Niu Lang na bakin ciki kwarai, har yana neman kashe kansa, tsohon bijiminsa ya yi magana cewa, ‘Mai gida, sai ka kashe ni, ka shiga cikin fatata, za ka iya yin shawagi.’ Niu Lang ba ya so ya kashe bijiminsa, amma bijimin ya yi ya yi har Niu Lang ya yarda. Domin Niu Lang shi ma ya sani, ba ya da sauran hanyar da zai bi domin ceton Zhi Nu. Shi ya sa tare da hawaye a cikin idanunsa, ya kashe tsohon bijimin.
Niu Lang ya shiga cikin fatan bijimin, ya dauki yaransa biyu, ya tashi zuwa can sama. Amma ba a yarda ya shiga cikin fadar sarkin aljanu ba. Sarkin aljanu ya ki yarda da shi da ya sadu da Zhi Nu.
Niu Lang da yaransa suna ta rokon sarkin aljanu, suka gurfana a gaban sarkin aljanu, suka yi kuka, har a karshe dai sarkin ya yarda da su sadu a cikin dan lokaci. Da Zhi Nu ta fito daga cikin gidan yari, ta ga mijinta da yaranta, ta ji murna kwarai da gaske, tana ta kuka, har ta kasa magana. Amma, lokaci ya wuce cikin sauri, an kama Zhi Nu, za a sake mai da ita cikin gidan yari. Niu Lang ya bi ta yana gudu, sauran kadan zai kama hannunta. Amma matan sarkin ta cire fin da ke cikin gashin kansa, ta shata layi a tsakanin Niu Lang da Zhi Nu. Sai layin nan ya zama babban kogi. Niu Lang da Zhi Nu, daya ya tsaya a gefe nan, daya ma a gefe can, suna hangen juna, amma ba za su sadu da juna ba. Daga baya, shekara da shekaru, Niu Lang da Zhi Nu ba su iya gamuwa da juna ba, ban da ran 7 ga watan Yuli a bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. A ran nan, tsuntsaye da yawa sun zo, sun kafa gada a kan kogin da fikafikansu domin Niu Lang da Zhi Nu da yaransu sun sadu da juna.