DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI
Wannan hatimin Annabtar yana daga cikin alamomi guda 3 wadanda suka janyo musuluntar Salmanul Farisi (ra).
Shi Salmanul Farisi ainihinsa mutumin Qasar Farisa ne. Wato IRAN. Mahaifinsa mai wadata ne. kuma Babbane agarin. kuma yana mutukar son Salmanun (rta).
Ya taso agidansu da kuma garinsu ya tarar suna bauta ma WUTA ne. Sai watarana Babansa ya aikeshi zuwa wata gonarsa, akan hanya sai yaga wasu Kiristoci suna Ibada achochinsu.
Sai yaga abin ya burgeshi. Don haka ya tsaya ya saurara. Sannan ya koma gida yana bayar da Labari yana cewa: "YAU NAGA WASU MUTANE SUNA IBADA, AMMA FA IBADARSU TAFI TAMU"
Da Babansa ya samu labari sai yasa aka daureshi Aka kulleshi acikin wani Daki. Aka sa mai tsaronsa.
Ana cikin hakane sai ya samu dama ya Kubce
Ya gudu wajen wadannan kiristocin. Yace su kwatanta masa garin da zaije ya samu mutanen kirki masu bin irin wannan addinin nasu.
Sai suka ce masa ya tafi Sham (Syria). Achan ne ya samu wani babban Pada na Kirista (nasara) ya zauna ya zama almajirinsa yana yi masa hidima tsawon wasu shekaru har zuwa lokacin da Padan zai rasu, Sai Salman ya tambayeshi cewa:
"INA SO KAYI MIN WASIYYAR GARIN DA ZAN SAMU WANI MUTUMIN KIRKI WANDA YAKE KAN WANNAN ADDININ?"
Sai ya turashi Izuwa wani gari zuwa wajen wani Pada. Anan ma haka yayi ta masa hidima har sai da ya cika. Shima da zai rasu sai da Salman yayi masa irin waccan tambayar.
Hakanan dai ya rika yawo daga wajen wannan pada izuwa wancan, daga Sham zuwa Mausul zuwa 'Umuriyyah ta Rum.
Har dai na Karshen cikinsu yace masa:
"Yanzu babu sauran wani mutum wanda yake kan ainihin koyarwar wannan addinin. Amma yanzu haka ma Ka iso lokacin bayyanar ANNABIN QARSHE. zai q haifeshi a Haramin Makkah amma zai yi hijira zuwa wani gari mai Qasar gishiri da kuma yawan Dabinai Don haka ka tafi chan wajensa"
"Yana da wasu siffofi guda 3 wadanda ba zasu buya agareka ba.
1. BA YA CIN SADAQA.
2. AMMA YANQ CIN KYAUTA.
3. YANA DA KHATIMIN ANNABTA ATSAKANIN KAFADUNSA".
Saboda haka Salman yana nan acikin wannan halin, Rannan sai ga wasu yahudawa wadanda suke zaune kusa da Madeena sunzo garin da yake.
Yace musu idan sun yarda zasu tafi dashi zuwa Madina, zai basu dukkan dukiyar da ya mallaka.
Awannan lokacin kuwa Salamanul Farisi mutum ne mai tarin dukiya da yawa.
Ga kudi, ga shanu, ga Rakumma, ga Tumaki.. Ance ko shanun ma sunfi 100.
Amma haka duk ya tattara ya basu. Don kawai yana so su kawoshi garin da zai hadu da Manzon Allah (saww).
To amma saboda rashin adalci irin na Yahudawa, bayan sun taho dashi akan hanya sai suka sayar dashi amatsayin Bawa.
Sai suka Sayar dashi ga wani mutum, shi kuma ya sayar dashi a kusa da Madeena. wani daga Yahudawan Banu Qurayzah ne ya sayeshi.
Amma awannan lokacin, Manzon Allah (saww) yana Makkah. bai yi hijira zuwa Madeena ba.
Don haka anan Salmanul Farisi ya zauna amatsayin Bawa, shekara da shekaru.
Watarana Ubangidansa yasa shi ya hau bishiya ya yanko masa Dabino. Yana kan dabinon sai Shi Maigidan nasa yayi wani Bako yazo wajensa acikin bacin rai da tashin hankali.
Yana ce masa:
"KAICON LARABAWAN NAN !! WAI KAJISU SUN TAFI QUBA'A SUN TARU AWAJEN WANI MUTUM SUNA CEWA WAI SHI ANNABI NE"
Sai Salmanul Farisi yaji wata irin Hajijiya ta kamashi. kamar zai fado Qas. Jikinsa yana rawa!!
Ya sauko yace musu:
"DON ALLAH ME KUKE FA'DA? SHIN WANNAN ANNABIN YA BAYYANA NE?? A INA YAKE?"
Nan take sai Ubangidan nasa ya Tsinka masa Mari!!
Yace masa:
"KAI KANA BAWA, INA RUWANKA DA WANNAN ZANCEN?"
Shi dai Salmanul Farisi bai yi Qasa agwiwa ba, yaci gaba da tuntubar labarin Manzon Allah (saww).
Har dai ya samu labarin cewa Manzon Allah (saww) yana chan a Quba'. (Wani Qauye ne kusa da Madeenah).
Sai ya nemi 'dan Dabinonsa ya rike. Sannan ya tafi wajen Manzon Allah (saww).
Daga zuwa sai ya same shi atsakiyar Sahabbansa suna zaune. Sai ya mika masa dabinon nan yace masa:
"GA SADAQAH na kawo muku ne don naga kun chanchanta."
Sai Manzon Allah (saww) yace ma Sahabbai "KU CI"
Amma fa Shi (saww) bai ci ba.
Salmanul Farisi ya fada (azuciyar sa) yace "Naga 'daya daga siffofin nan"
Washe gari ma sai ya sake dawowa da wani dabinon. Ya miko ma Manzon Allah (saww). Yace : "GASHI WANNAN KYAUTA CE NA KAWO MAKA DON NAGA KAMAR BAKA CIN SADAQAH"
Sai Manzon Allah (saww) yq karba da hannunsa mai albarka. Ya bude dabinon ya fara ci sannan ya mika wa Sahabbansa (rta).
Da Salmanul Farisi (rta) yaga haka sai yace:
"NAGA NA BIYU"
Daga nan sai Salmanul Farisi ya sake dawowa. Adaidai lokacin nan Manzon Allah (saww) yana wajen Makabartar Baqee'a. ya tafi janazar wani daga cikin Sabbansa (rta).
Salmanu yace:
"Sai na kasance ina bin bayansa ina duddubawa ko zan ga cikon alama ta ukun nan wacce Malamina ya gaya min?"
Shi kuwa Manzon Allah (saww) yana sanye da wani Mayafi.
Da yaga ina binsa abaya-abaya sai kawai ya tube mayafin. Yace min:
"SALAMANU KO KANA SO KAGA WANNAN ABUN NE?"
Salamanu yace "Sai naga wannan KHATIMIN ANNABTAR ABAYAN KAFADARSA. KAMAR GIRMAN QWAN TATTABARA"
"SAI NA RUNGUMESHI INA KUKA, INA SUMBARTAR KHATIMIN ANNABTAR INA KUKA"
Sai Manzon Allah (saww) yace min:
"JUYO YA SALMANU KA BANI LABARI"
Nan take sai na bashi labarina tun daga farko har Qarshe.
ALLAHU AKBAR!!
Nan zqmu tsaya, Sai nan gaba zamu dora a kashi na uku IN SHA ALLAHU.
Don neman Qarin bayani akan wannan aduba tarjamar Sayyiduna Salman Alfarisy cikin wadannan litattafan:
★ SIYARU A'ALAMIN NUBALA
★ USUDUL GHAABAH.
★ TAREEKHUL KABEER.
★ ALBIDAYAH WAN NIHAYAH.
★ SIFATUS SAFWAH.
★ RIJALUN WA NISA'UN HAULAR RASUL (SAWW).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.