TAMBAYA TA 1649
******************
Malam Allah ya biyaka bisa ayyukan alkhairi da kakeyi mana. Malam tambaya nake dashi kamar haka
1.nine Ina cikin karatu sai ga wani Karamin kwaro ya shige cikin makogorona na hadiye ba da son raina ba. Yaya hukuncin examine?
2. Nayi gyatsa ne sai naji danshin abinci a makogorona yabi ya koma.to shima malam yaya hukuncin axumina? Assalamu alaikum
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Acikin dukkan yanayin nan guda biyu wadanda ka ambata, AZUMINKA YANA NAN BAI KARYE BA. Duk wanda Kwaro ya shige masa ta makogoro ba tare da saninsa ba, to azuminsa yana nan.
Hakanan wanda yaji alamar damshin abinci acikin makogoronsa, amma bai zo cikin bakinsa ba ballantana ya tofar. Shima azuminsa yana nan.
WALLAHU A'ALAM.