A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sababbin manyan jami'an tsaron kasar. Shin kun san tarihin su?
Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin
Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin shi ne sabon hafsan hafsoshin tsaron Najeriya.
Shi dan asalin jihar Ekiti ne da ke kudu maso yammacin kasar.
Kafin a nada shi a kan wannan mukami, shi ne shugaban cibiyar bayar da umarni ta sojin Najeriya da ke birnin Minna na jihar Naija.
Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai
Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai shi ne sabon hafsan dakarun sojin kasa na Najeriya.
Buratai dan asalin jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kafin nadin sa, Buratai shi ke jagorantar rundunar tsaro ta hadin-gwiwa wacce ke da hedikwata a birnin Ndjamena na kasar Chadi.
Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin ne suka kafa rundunar domin yaki da 'yan ta'addan da ke yankinsu.
A baya dai, Manjo Janar Buratai ya yi aiki a matsayin Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin Najeriya da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers, sannan ya taba zama Kwamandan makarantar horas da sojin kasa da ke Jaji, jihar Kaduna.
Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas
Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas shi aka nada a matsayin hafsan dakarun sojin ruwa.
Ibok-Ete Ekwe Ibas dan asalin jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya ne.
Ya shiga makarantar horas da sojoji, watoNigerian Defence Academya shekarar 1979, kuma ya zamaSub-Lieutenanta shekarar 1983.
Cikin mukaman da ya rike kafin wannan mukamin har da: shugaban makarantar sojin ruwa da shugaban ma'aikatan da ke samun horon sojin ruwa da shugaban gudanarwa na sojin ruwa, da kuma shugaban tsare-tsare na sojin ruwa.
Haka kuma ya rike mukamin babban jami'in kamfanin sojin ruwa naNavy holding limited.
Air Vice Marshal Sadique AbubakarAir Vice Marshal Sadique Abubakar shi ne sabon babban hafsan sojin sama.
Shi dan asalin jihar Bauchi ne.
Kafin nadin sa ya taba zama shugaban sashen da ke tabbatar da ingancin aiki na rundunar sojin sama da kuma jami'in kula da sadarwa da Kwamandan horas da sojin sama na Najeriya.
Air Vice Marshal Monday Riku Morgan
Air Vice Marshal Monday Riku Morgan shi aka nada a matsayin babban jami'in kula da bayanan sirri na tsaro a kasar.
Air Vice Marshal Morgan dan asalin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ne.
A shekarar 1982 ne ya zama sojin sama.
Cikin mukaman da ya rike har da: Kwamandan Sojin Sama da ke kula da tsare-tsare.
Manjo Janar Babagana MongunoManjo Janar Babagana Monguno shi ne sabon mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.
An haifi Monguno a garin Monguno da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya shiga makarantar horas da sojoji, watoNigerian Defence Academy.
Kafin ya yi ritaya daga soji, ya rike mukamai da dama, cikin su har da: Kwamandan rundunar tsaron shugaban kasa, mataimakin kwamanda a kwalejin koyon aikin soji, babban mai kula da sha'anin sirrin soji.