Tsohon kociyan Super Eagles Stephen Keshi ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Nigeria da ta biya shi diyyar £3.2m kan sallamarsa da ta yi daga aiki.
A farkon watan Yuli ne NFF ta kori Keshi daga aikin horas da tawagar kwallon kafar kasar ta kuma maye gurbinsa da Sunday Oliseh.
Hukumar ta NFF ta samu Keshi da laifin zawarcin aikin horas da tawagar kwallon kafar Ivory Coast bayan kuma yana da yarjejeniya da ya kulla da hukumar.
Keshi ya aike wa da NFF wasika ta hannun lauyansa, a inda ya bukaci a biya shi kudin kan bata masa suna da aka yi.
Sai dai kuma mahukuntan NFF sun ce diyyar da Keshi ke nema a biya shi ba ta da tushe balle makama, kuma ba za a tilasta musu biyan kudin ba.
Duniya ta fahimci cewar Keshi na kokarin kare martabarsa a fagen tamaula, bayan da kwamitin ladabtarwa na NFF ya zargi kocin da laifuka da dama.
Har yanzu Keshi bai kai batun kotu ba, amma yana fatan a gano bakin zaren cikin ruwan sanyi.