TAMBAYA TA 1641
********************
Assalamu Alaikun da fatan Mallam yana lafiya, ya azumi, Mallam ina daya daga cikin 'Dalibin wannan zauren nasha aiko da tanbaya amma bana samun amshoshin daga Gareka, Mallam Dan Allah inaso a amsa mini tambayoyin nawa guda biyu2, Mallam mutun ne ya dauki azumi sai ya kwanta barci sai yayi mafarki ya sadu da Mace jima'i har maniyyi ya fito masa, Mallam ya mazaunin azuminsa yake, Zaici gaba da cin abinci ne, ko zaiyi kamun baki daga baya ya biya azumin, ko Azuminsa yana nan. Ga daya tambayar Mace zata iya wankan Janaba ba sai ta ji'ka gashin kanta ba.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Wanda yayi mafarkin jimawa da azumi, to azuminsa yana nan bai karye ba. Ko ya fitar da wani abu acikin mafarkin ko bai fitar ba. Sai dai wanka kawai zaiyi yaci gaba da sauran ibadunsa.
2. WAJIBI ne mace ta game dukkan jikinta da ruwa yayin wankan haila ko na janaba. Kanta ma jikinta ne. Don haka wajibi ne ta tabbatar cewa ruwan yana ratsawa ta cikin gashinta
WALLAHU AAAMEEEN