TAMBAYA TA 1653
*******************
Assalamu Alaikum, malam ya Azumi da jama'a Allah ya baka ladan abinda kake yasa Jannatul firdausi ce makomarka. Malam dan Allah dan Albarka wannan wata ka taimaka ka amsa min tmby ta, mlm ynz shekaruna 11 da aure da yara 4 to mlm sai naje sai naje nayi planing jinin haila na yakan zo ba zai dauke ba har sai yayi kwanaki goma sha zuwa 15 shin malam yaya azumi na yake?
Amma kaji dalilin da yasa nayi (Family Planning) shine mlm, muna zaune a lagos ga kudin haya da makarantar yara ga kudin abinci sai godiyar Allah, Wallahi mlm mai aiki ma inka dauka babu wanda zata maka kasa da dubu goma,sai sama, ina neman shawarka, kuma na Dade ina tare da wannan zaure. Allah ya kara basira. pls mlm pls hide my id. may Allah reward u with jannatul Firdaus.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Shi dai Qayyade iyali (wato family planning) ya rabu kashi biyu ne kamar haka:
1. Qayyade haihuwa na dindindin (wanda har abada mutum ba zai saje haihuwa ba) - Wannan HARAMUN ne. kuma babu sabanin malamai akan haramcinsa. Sai dai idan likitoci ne suka gaya ma mace cewar idan ta sake daukar ciki, zata iya rasa ranta. To wannan ya halatta tayi, idan chutar ba ta warkewa bace.
2. Qayyade haihuwa zuwa wani lokaci : Wannan shi ya halatta ayishi idan har akwai wani Kakkarfan dalili (ba wai don tsoron talauci ba).
Kuma dole sai da shawarar likitoci domin a tabbatar cewa babu wata chutarwa acikin ALLURAR da za'ayi. amma idan akwai chutarwa, to bai halatta ayi ba. Tunda Allah yace:
"KAR KU JEFA HANNUWANKU ZUWA GA HALLAKA".
To wannan family planning din naki, mutukar dai yana haddasa miki zubar jini mai yawa, ko kuma rikicewar jinin al'adarki, to hakika zai iya haifar miki da manyan matsaloli a lafiyar jikinki. Ayanzu ko nan gaba. Don haka barinsa zai fi alkhairi gareki.
Musamman tunda dalilan naki ba masu Qarfi bane. Ba wai kina yi don kiwon lafiyarki bane. A'a kina yi ne don tsoron talauci. Shi kuwa Ubangiji ya riga ya tsara ma kowanne mai rai arzikin da zai samu tun kafin yazo duniyar ma.
Shi kuwa hukuncin azuminki, Mutukar dai jininki na hailar nan bai tsallake kwana sha biyar ba, yana nan amatsayin JININ HAILA. ba zakiyi sallah ko azumi ba.
Amma idan ya haura kwana 15, to zakiyi wanka ki ci gaba da sallah da azumi, da kuma mu'amala da Mijinki.
WALLAHU A'ALAM.