TAMBAYA TA 1650
********************
Assalamu Alaikum Malam da fatan kana lafiya Allah ya saka maka da Alkhairi Ameen. Malam a taimaka a amsa min tambayoyina kamar haka:
1.Malam mutum ne yake amfani da wayarsa yayi hacking din mobile network suna bashi 2GB,4GB etc yana sayarwa mutane yana amfani da kudin. Menene hukuncinsa a musulunci? Kuma menene hukuncin wadanda ya ciyar dasu abinci da wannan kudin?.
2.Malam a cikin post dinka ka taba yin bayani akan wata sallar nafila da kuma adduo'in da za'ayi domin samun biyan bukata da yayewar matsala malam nima inaso a taimaka min. Ka huta lafiya daga wani bawan Allah
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
1. AMSAR TAMBAYARKA TA FARKO: Hakika Wannan hacking din da suke yi, yana daga cikin abinda ake kira Ta'addanci, ko kuma satar fasaha.
Musulunci ya bada damar cewa duk wanda ya Qirkiri wani abu, ko kuma ya wallafa wani littafi, to yana da cikakkiyar damar COPY RIGHT akan abun. Don Haka bai halatta wani yayi amfani da abun ta wata hanya wacce bada izinin mai abun ba.
Kampanonin Network suna kashe kudade wajen samar da network Service tare da gudanar da sauran harkokinsu. Don haka bai halatta wani ya rika yin wasu dabaru yana yi musu satar fasaharsu, yana sayarwa yana ci da guminsu ba.
Acikin wani Hadisi Manzon Allah (saww) ya kawo zancen wani mutum mai yin addu'a, alhali abincinsa na haram ne, abin shansa ma na haram ne, Suturarsa ma ta haram ce, kuma da haram din aka ciyar dashi har zuwa girmansa. Manzon Allah (saww) yace TA YAYA ZA'A AMSHI ADDU'ARSA!.
Kum yace Allah ya Umurci Muminai da irin umurnin da yayi ma Manzanninsa. Yace musu "YA KU MANZANNI! KUCI DAGA TSARKAKAN ABUBUWA, KUMA KUYI AIKI NAGARI".
kuma yace ma Muminai : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KUCI DAGA TSARKAKAN ABUBUWAN DA MUKA AZURTAKU DASHI".
Kaga kenan bai halatta mutum ya rika ciyar da iyalansa da kudaden da ya samo ta hanyar Haram ba. Yin haka tamkar yana rusa ingantuwar tarbiyyar iyalansa ne.
2. Dangane da tambayarka ta biyu kuwa, ka duba tambaya ta 1552 zaka samu amsarka awajen.
WALLAHU A'ALAM.