ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA SUN BAYYANA A FACEBOOK DA WHATSAPP.
Dalilin da yasa na fadi wannan maganar shine akwai wata tambaya guda daya wacce asatin nan kadai kusan mutum goma ne sukayi min ita. Kuma na tabbata kun ganta a facebook da WHATSAPP.
Wannan tambayar ita ce:
"WACCE MACE CE MIJINTA ANNABI, YAYANTA ANNABI, BABANTA ANNABI, KUMA DANTA MA ANNABI?".
- Shin don Girman Allah mainene amfanin irin wannan tamabayar??
- Shin idan ka sani, wanne amfani zatayi maka?
- Shin zaka chutu ne idan baka, sani ba??
Manzon Allah (saww) yace idan alkiyamah ta kusa, za'a samu mutane MASU YIN TA'ADDANCI ACIKIN ADDU'A, Awani hadisin kuma yace zasu rika yin TA'ADDANCI ACIKIN TAMBAYA...
Awani hadisin kuma yace: "MUTANE BA ZASU RIKA DAMUWA DA SHA'ANIN ADDINI BA".
Manzon Allah (saww) yayi gaskiya. Domin kuwa yawancin masu yin Wadannan tambayoyin ta'addancin ba zaka jisu suna tambayarka akan Sallah ko Zakkah ko azumi ko aikin Hajji ba.. Sai dai irin wadannan tambayoyin da ba, zasu amfanesu ba..
Ba zaku tambayi mutane akan tarihin Annabinku (saww) ko Ahalin gidansa ko Sahabbansa ba, Sai ku rika kirkiro wani abu marar tushe kuna ta tambayar mutane!!
NOTE: Duk wanda ya sake yi min irin wannan tambayar ta WHATSAPP zanyi blocking dinsa nan take Instantly.
ZAUREN FIQHU yayi izinin ayi sharing din post din nan ta Facebook da WHATSAPP saboda masu irin wannan ta'addancin su dena.