Gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar ba su ce ko uffan ba, kwanaki biyu bayan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a wasu kauyukan jihar Borno, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 150.
Mayakan kungiyar sun hallaka masallata 97 a kauyuka guda uku a karamar hukumar Kukawa bayan da suka jira mutanen suka idar da Sallah a ranar Laraba.
Wani mutumin garin Kukawa, Babami Alhaji Kolo wanda ya tsere zuwa Maiduguri ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan Boko Haram sama da 50 ne suka yi wa kauyen tsinke.
A ranar Talata kuma a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Monguno 'yan Boko Haram din sun hallaka mutane 48 a cikin dare sannan suka kona gine-gine da dama a kauyukan.
Dan majalisa da ke wakiltar yankin, Mohammed Tahir Monguno ya shaida wa BBC cewa tun a ranar Talata mayakan Boko Haram din suka kaddamar da harin a lokacin mutane suna Sallah.
Wani mazaunin garin Monguno a hirarsa da BBC ya ce "Mutanen da aka kashe sun fi 50. Mutane na Sallah, suka jira su sannan suka raba maza da mata kafin su ('yan Boko Haram) hallaka mazan."
Wannan harin shi ne mafi muni da Boko Haram ta kaddamar tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a watan Mayu.
Gabanin kai hare-haren mataimakin shugaban Nigeria, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN ya kai ziyara birnin Maiduguri na jihar Borno domin jajinta wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Title :
Gwamnati ta yi shiru kan kisan da Boko Haram ta yi a Borno
Description : Gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar ba su ce ko uffan ba, kwanaki biyu bayan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a wasu kauyukan...
Rating :
5