Wata majiya a fadar shugaban Nigeria ta shaidawa manema labarai cewar, an fara gudanar da bincike domin tantance sahihanci wadansu mutane da suka yi ikirarin suna wakiltar kungiyar Boko Haram ne kuma a shirye suke su tattauna da gwamnati.
Majiyar ta jaddada cewar gwamnati ba ta fara shawarwari da kungiyar Boko Haram ba, amma ba ta son ta yi kuskure na tattaunawa da mutanen da ba sa wakiltar kungiyar.
A kwanakin baya, Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewar a shirye gwamnatinsa ta ke ta tattauna da 'yan kungiyar Boko Haram idan har za ta iya tantance sahihanci duk wani wanda ya yi ikirarin yana wakiltar kungiyar.
A lokacin hirarsa da CNN a makon da ya gabata a Amurka, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta kore yiwuwar tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram ba, dangane da sakin 'yan matan sakandare na Chibok sama da 200 da kungiyar ta yi garkuwa da su tun a watan Afrilun 2014.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria.