Gwamnatin Nigeria ta ce ana daukar matakai na binciko tare da hukunta duk wasu dake da hannu a wani haramtaccen gidan radio mai suna Radio Biafra dake watsa shirye shirye a wasu yankuna na kudu maso kudancin kasar.
Haka kuma gwamnatin ta musanta wata murya da ta ce gidan rediyon ya yi ta yayatawa wanda yayi ikirarin cewa hira ce da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya shaida wa manema labarai, inda gidan rediyon ya ce Shugaba Buharin ya furta wasu kalamai dake nuna kin jinin 'yan kabilar Igbo.
Malam Garba Shehu mataimaki na musammman ga shugaban kasa kan yada labarai,ya shaidawa manema labarai cewa ' a inda duk aka sake jin a bullo da wata tashar rediyo haramtacciya, ana yada shirye shirye na wargaza Nigeria ko wanda zai sabawa doka, gwamnati za ta dauki kyakyawan mataki a kan kowanene ya mallaki wannan tauraron dan-Adam
Garba Shehu ya kara da cewa 'an kira su, an kuma ja musu kunne, an ce musu su je su toshe wannan haramtaccen gidan rediyo, idan ba haka ba za su ga bacin ran gwamnatin Nigeria'.
'Tabbacin da suka bada shi ne daga ranar Laraba da daddare ba za a kara jin duriyar gidan rediyon Biafra ba' in ji Garba Shehu.