Assalamu alaikum Jama'a. Kamar yadda ZAUREN FIQHU ya dauki alkawari cewa zai kawo muku wasu daga cikin fa'idodin Habbatus sauda, ga alkawarin zamu cikashi insha Allahu kamar haka:
1. MAGANIN SAURO DA SAURAN QWARI MASU CUTARWA: asamu garin Habbatus sauda, aturarashi daidai Misali. Insha Allah duk wasu Qwari masu cutarwa kamarsu Kyankyaso, sauro, tsaka, Qadangare, Kunama, duk zasu fice daga dakin.
2. Irin yaran nan wadanda zaka ga an haifesu basu da lafiyar kwakewalwa sosai, wato MUGAFFAL kenan. Asamu Man habbatus Sauda atofa Fatiha 1, ayatul kursiyyu 11, Qul huwallahu da falaki da nasi Qafa 3 sannan arika bashi yana shan cokali guda kullum, kuma arika shafa masa duk jikinsa. Musamman ma kayinsa. Insha Allahu zai samu gyaruwar Kwakwalwa da kuma basira.
3. MATA MASU JUNA BIYU: asamu garin Habbatus Sauda cokali 7, citta da kanunfari cokali 2, ahada cikin zuma kofi guda da rabi. Arika shan cokali 1 safe da rana da yamma.
Insha Allahu zata samu kuzari da Qarfin jikinta. Kuma zata samu kariya daga cututtuka da ita da jaririnta. Kuma zata samu saukin nakuda.
4. FITAR MAZIYYI: samarin da suke fama da matsalar fitar maziyyi ba bisa qa'ida ba, idan suna shan Man habbatus Sauda ko garinta tare da zuma insha Allahu zai dena zubo musu ba bisa ka'ida ba.
5. TSUTSAR CIKI: habbatus Sauda tana maganin ciwon kai idan ana shafawa. Tana maganin ciwon ciki idan ana shanta sosai. Kuma tana narkar da Tsakuwar Qoda idan ana shanta da zuma.
Allah yasa mu dace.
DAGA ZAUREN FIQHU