Kimanin yara dubu biyar ne suka zamo marayu a Laberiya sakamakon kisan iyayensu da cutar ebola ta yi.
Mafi yawancin marayun sun rasa mai kula da su saboda kyamar su da ake yi bayan da iyayensu suka rasu.
Al'amarin ya fi kamari ga yaran da suka kamu da cutar ta ebola amma suka warke.
Kafin barkewar cutar ta ebola dai kasar ta Laberiya tana da marayu kimanin dubu daya ne kacal amma yanzu abin da kara karuwa ne.