A Najeriya, jami'an hukumar tsaro na farin kaya SSS sun yi karin haske kan dalilin da ya sa suka kai samame tare da cafke tsohon mai bai wa gwamnatin Najeriya shawara kan sha'anin tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya a makon da ya wuce.
A wata sanarwa da ta fitar, Hukumar tsaron SSS tace ta kai wananan samame ne domin samun bayanan sirri da ta yi na cewar tsohon mai ba shugaban Nigeria shawara kan sha'anin tsaro na kulle-kullen shirya wa kasar wata makarkashiya.
Sanarwar ta ci gaba da cewar an yi tataburza da Kanar Dasuki kafin ya bar su shiga gidansa da ke unguwar Asokoro a Abuja, dan gudanar da bincike, duk kuwa da cewa sun gabatar da takardar da ke nuna an ba su izinin yin wannan aiki.
Sanarwar ta ce an yi nasarar samun manyan motocin alfarma har guda 12, 5 daga cikinsu harsashi baya huda su, da manyan bindigogi masu sarrafa kan su guda 7, da wasu mujallu da suka danganci aikin soja,.
Ka na kuma Kanar Dasukin ya gagara gabatar musu da takardun shaidar mallakar wadannan motoci.
Hukumar ta diga ayar tambaya kan cewar ko me Kanar Dasuki yake yi da motoci irin wannan a matsayin sa na tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Nigeria? Haka kuma bai bada baynin wadannan kayayyaki ba a lokacin da aka sauke shi.