‘Yan sandan Farin kaya SSS sun bayyana dalilin da ya sa suka yi wa tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara Sambo Dasuki dirar mikiya a gidajensa da ke Abuja da Sokoto a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar bayan kammala binciken kwa-kwaf a gidajensa.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar dauke da sa hannu jami’inta Tony Opuiyo bayan sakin Sambo Dasuki daga daurin Talala da jami’anta suka yi ma sa na tsawon awanni 24, hukumar ta ce ta samu manyan makamai da motoci masu sulke 12 ciki har da na hawa masu tsada wadanda harsashe ba ya iya bulawa guda biyar.
Hukumar tsaron ta SSS ta fadi a cikin sanarwar cewa ta kai wa dasuki farmaki ne saboda wani zargin da ta alakanta na kulle kullen cin amanar kasa, don haka Jami‘anta suka abka wa gidajensa a Abuja da Sokoto domin gudanar da binciken kwa-kwaf akansa.
Hukumar tace binciken ya ja lokaci saboda Dasuki bai ba jami’anta hadin kai ba a gidansa da ke Asokoro, lamarin da ya sa aka shafe tsawon sa’o’i ana bincike.
Hukumar tace ba don kwarewar jami’anta ba da an yi gumurzu tsakaninsu da sojojin da ke tsaron gidan Dasuki, har sai da babban hafsan sojin Najeriya Manjo Ganar Buratai ya higa tsakani,
Bayan sakinsa daga daurin talala a gidansa, Sambo Dasuki ya bayyana rashin jin dadinsa musamman haramta ma shi zuwa Sallar idi, tare da shan alwashin kalubalantar matakin a kotu saboda ta ke ma shi hakki da aka yi.
A cikin sanarwar, hukumar SSS tace a sani cewa Sambo Dasuki ya yi ritaya yana Kanal don haka baya da ‘yancin sojoji su yi gadin gidansa, kuma tun lokacin da aka sauke shi daga mukamin mai ba shugaban kasa shawara ya kamata sojoji su fice daga harabar gidansa.