Chelsea ta dauki mai tsaron raga Asmir Begovic daga Stoke City kan kudi da ake hasashen cewa sun kai fam miliyan 8.
Golan mai shekaru 28, dan kasar Bosnia-Hercegovina zai zauna a Stamford Bridge tsawon shekaru hudu.
Stoke ta yi kokarin Golan ya kammala kwantiragin shekara daya da ya rage masa amma sai ya nuna yanason ya koma Chelsea
Begovic wanda ya koma Stoke City a shekarar 2010, ya zama dan kwallo na biyu da Chelsea ta dauka, bayan Radamel Falcao.
Kuma mai tsaron ragar zai maye gurbin Petr Cech ne wanda ya koma Arsenal da Murza leda.
Title :
Chelsea ta dauki Asmir Begovic
Description : Chelsea ta dauki mai tsaron raga Asmir Begovic daga Stoke City kan kudi da ake hasashen cewa sun kai fam miliyan 8. Golan mai shekaru 28, d...
Rating :
5