A yau Lahadi ne, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Amurka domin ganawa da shugaba Barack Obama.
A na dai sa ran cewa ziyarar za tafi mayar da hankali kan yadda kasar ta Amurka za ta taimaka wa Najeriya wajen dakile ayyukan Boko Haram da kuma inganta tattalin arzikin Najeriyar.
Har wayau, a na ganin cewa ziyarar za ta dasa dan-ba wajen sake yi wa alakar kasashen biyu garanbawul.
A baya dai dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami a inda har Amurka ta sanya wa Najeriyar takunkumin sayen makamai bisa zargin rashin keta hakkin bil'adama.
A na sa ran shugaban kasa Buhari zai kwashe kwanaki hudu a Amurkar yayin ziyarar.