A yau Litinin ne, ake sa ran shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai gana shugaba Barack Obama na Amurka a yayin ziyarar aiki da ya kai kasar.
A na dai sa ran cewa ziyarar za tafi mayar da hankali kan yadda kasar ta Amurka za ta taimaka wa Najeriya wajen dakile ayyukan Boko Haram da kuma tallafawa Najeriyar wajen aniyarta na yaki da rashawa da cin-hanci.
Har wayau, a na ganin cewa ziyarar za ta dasa dan-ba wajen sake yi wa alakar kasashen biyu garanbawul.
A baya dai dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami a inda har Amurka ta sanya wa Najeriyar takunkumin sayen makamai bisa zargin keta hakkin bil'adama.
A na sa ran shugaban kasa Buhari zai kwashe kwanaki hudu a Amurkar yayin ziyarar.