Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya
amince da nadin sabobbin manyan jami'an
tsaron kasar.
A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban
kasar, Femi Adesina ya fitar, ta ce an nada
Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin a
matsayin babban hafsan hafsoshin tsaron
kasar.
Sai kuma Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai a
matsayin hafsan dakarun sojin kasa na
kasar.
Sanarwar ta ce sabon hafsan dakarun sojin
ruwan kasar shi ne Rear Admiral Ibok-Ete
Ekwe Ibas a yayinda aka nada Air Vice
Marshal Sadique Abubakar a matsayin
babban hafsan sojin saman kasar.
Sauran wadanda shugaba Buhari ya nada a
bangaren tsaron, sun hada da Air Vice
Marshal Monday Riku Morgan a matsayin
babban jami'in kula da bayanan sirri na
tsaro a kasar da kuma Manjo Janar
Babagana Monguno a matsayin mai bai wa
shugaban kasa shawara a kan harkokin
tsaro.
'Kora'
A ranar Litinin ne aka sanar da korar
manyan jami'an tsaron kasar a wani mataki
da ake kallo na yunkurin Shugaba Buhari na
yaki da kungiyar Boko Haram.
Wadanda aka kora su ne: Air Marshal Alex
Badeh, Janar Kenneth Minima da Rear
Admiral Usman Jibrin da kuma Air Vice
Marshal Adesola Amosun.
An dade ana saran shugaba Buhari zai kori
manyan hafsoshin tsaron a daidai lokacin
da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da
kaddamar da hare-hare a cikin kasar.
A cikin kwanaki goma da suka wuce an
kashe mutane fiye da 220 a Nigeria
sakamakon hare-haren Boko Haram
Title :
Buhari ya nada sabbobin jami'an tsaro
Description : Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya amince da nadin sabobbin manyan jami'an tsaron kasar. A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban...
Rating :
5